1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An gana tsakanin Ibrahim Gambari da Aung San Suu kyi

Wakilin MDD na musamman akan harkokin siyasa Ibrahim Gambari ya gana da shugabar adawa ta Myanmar Aung San Suu Kyi. Shugabannin gwamnatin mulkin sojin kasar suka ba shi izinin kai mata wata gajeriyar ziyara. A ranar alhamis mista Gambari ya isa birnin Yangon, inda ya gana da Suu kyi a gidan sauke baki na gwamnati, to amma ba´a ba da bayanin batutuwan da suka tattauana kai ba. An shirya wannan ziyarar ce gabanin wani taron kwamitin sulhu wanda a karon farko a wannan shekara aka gaiyaci Myanmar da ta shiga muhawwara da za´a yi game da tabarbarewar halin siyasa da na kare hakkin ´yab adam a cikin kasar.