An gana tsakanin Hu JinTao da Georges Bush a fadar White House
April 20, 2006Talla
A ci gaba da ziyara aikin da ya kai Amurika, shughaban ƙsar China Hu Jin Tao, ya gana a ranar yau, da shugaba Georges Bush a fadar White House.
Tawagogin sun tantana a game da ba tutuwan da su ka shafi cinikaya tsakanin China da Amurika, da kuma harakokin diplomatia.
Bush,yayi anfani da wannan dama, inda yayi masanyar ra´ayoyi a game da matsalar rikicin makaman nukleyar kasar Iran ya kuma nemi goyan bayan China daukar matakan ladabtar da hukumominTeheran.
A jawabin a na marhabin a zuwa,shugaba Bush,ya yaba hulɗoɗin da su ka hada Amurika da China.
Ganawa da shugaba Bush,shine matakin karshe, na wannan ziyara farko da shuga ba Hu Jin Tao ya kai a fadar White House.