An gana tsakanin Bush da Al-Maliki | Labarai | DW | 25.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An gana tsakanin Bush da Al-Maliki

Amirka ta ce tana shirin mayar da karin sojojinta a birnin Bagadaza. Shugaba GWB ya nunar da haka bayan ganawar da yayi da FM Iraqi Nuri Al-Maliki a birnin Washington. A wani taron manema labarai na hadin guiwa da FM na Iraqi, Bush ya ce al-Maliki da kwamandan dakarun Amirka a Iraqi janar George Casey sun amince da tsugunar da karin sojojin Amirka da na Iraqi a Bagadaza nan da makonni kalilan masu zuwa. Bush ya ce ana shirye shiryen yiwa tsarin harkokin tsaron birnin kwaskwarima.