1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An gana tsakanin Abbas da shugabanni Hamas

A jiya aka gana tsakanin shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas da shugabannin kungiyar Hamas inda suka tattauna akan kafa sabuwar gwamnati. Tattaunawar dai ita ce ta farko tun bayan da kungiyar Hamas ta lashe zaben ´yan majalisar dokokin Falasdinawa. A gun taron Abbas da wakilan kungiyar ta masu kishin Islama sun amince majalisar dokoki ta fara zamanta a ranar 16 ga watannan na fabrairu. Wani kakakin Hamas ya ce kungiyar zata karbi ikon dakarun tsaron Falasdinu. Ana sa ran cewa Abbas wanda kungiyar sa ta fatah ta sha kaye a zaben, zai bukaci duk wata gwamnati da Hamas zata yiwa jagoranci, ta girmama yarjeniyoyin da aka kulla tsakanin Isra´ila da hukumar mulkin Falasdinawa.