An gana tsakanin Abbas da Misis Rice a garin Jericho | Labarai | DW | 30.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An gana tsakanin Abbas da Misis Rice a garin Jericho

Shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas da sakatariyar harkokin wajen Amirka C-Rice sun yi kira da a fadada shirin tsagaita wuta tsakanin Isra´ila da Falasdinawa daga Zirin Gaza zuwa Gabar Yamma da Kogin Jordan. Rice wadda a halin yanzu ta ke rangadin yankin GTT da nufin karfafa yarjejeniyar zaman lafiya, ta yabawa shugaba Abbas bisa rawar da ya taka wajen cimma shirin tsagaita wutar da kuma kokarin da yake yi wajen kafa gwamnatin hadin kai da kungiyar Hamas. To sai dai a nasa bangaren Abbas cewa yayi tattaunwar kafa gwamnatin hadin kan ta cije.