1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

AN GABATAR WA MAJALISA KUNDIN TSARIN DOKOKIN KAYYADE SHARUDDAN TURA DAKARUN JAMUS ZUWA KETARE.

YAHAYA AHMEDMarch 25, 2004

A cikin shekarar 1994 ne kotun kundin tsarin mulkin kasa ta tarayya, ta yanke hukunci kan tura dakarun Jamus zuwa aikin kare zaman lafiya a kasashen ketare. Tun wannan lokacin ne kuma, gwamnatin tarayya ke bukatar amincewar majalisar dokoki, kafin ta tsai da shawarar girke sojojin kasar a ketare.

https://p.dw.com/p/Bvl3
Sojojin rundunar Bundeswehr ta Jamus, a birnin Kabul - Afghanistan.
Sojojin rundunar Bundeswehr ta Jamus, a birnin Kabul - Afghanistan.Hoto: AP

Abin da gwamnatin tarayya ke nema dai, shi ne samun damar tura dakarun rundar sjoin Bundeswehr zuwa ketare ba tare da huskantar wani dogon turanci daga Majalisar dokoki ba. Bisa kundin dokar da gwamnatin hadin gwiwa ta jam’iyyun SPD da Greens, ta gabatar wa majalisar dai, nan gaba, ba sai ma’aikatar tsaro ta tarayya ta nemi izinin majalisar, kafin ta tura wani dan karamin rukuni na sojojinta zuwa ketare, don ya gudanad da aikin kare zaman lafiya karkashin laimar Majalisar dinkin Duniya ba.

Sanad da majalisar kawai ta wadatas. Amma `yan majalisar za su iya kiran taron gaggawa, don tattauna batun idan suka ga hakan ya dace. Idan ko dakaru da yawa ne za tura ketaren, to nan, sai majalisar ta ba da amincewarta tukuna, za a iya tura su.

A kasashe da dama dai, gwamnatoci ne ke tsai da shawarar tura dakarunsu zuwa ketare, ba majalisa ba. Amma a nan Jamus, majalisar na da iko na musamman wajen yi wa wasu manufofin gwamnati babakere. A shekaru 10 da suka wuce ne, kotun kundin tsarin mulkin kasa ta tarayya ta gabatad da wasu kudurorin da ya kamata a yi la’akari da su kafin a dau matakin tura dakarun Jamus zuwa ketare. Amma wadannan kudurorin ba dokoki ba ne. Sabili da hakan ne kuwa, ya zamo wajibi a sami dokar da za ta kayyade sharuddan a suka shafi wannan batun.

Jam’iyyun adawa dai na ganin cewa, bai kamata a rage angizon da majalisar dokoki ke da shi kan wannan lamarin ba. Sabili da haka ne kuwa, jam’iyyar FDP, ta gabtar da nata kundin don a yi muhawara a kansa a majalisa. A ganinta dai, ko yaushe za a tura dakarun Jamus zuwa ketare, to kamata ya yi a kafa wani kwamitin da zai yi nazarin halin da ake ciki a kassar da za a tura su, ya kuma ba da shawarar tura su ko kuma hana yin hakan. Kamar yadda wani dan majalisa na jam’iyyar, Jörg van Essen, ya bayyanar:-

"Idan aka kafa wannan kwamitin, to zai iya ba mu haske kan halin da ake ciki a ketaren, kafin a tsai da shawarar tura dakarun. Hakan kuma zai karfafa angizon da Majalisa ke da shi. Wannan dai shi ne gurinmu."