An gabatar da tuhumar Fillion a hukumance
March 14, 2017Talla
An gabatarwa da dan takarar shugabancin kasar Faransa Francois Fillion tuhume tuhumen da ake masa kan zargin amfani da dukiyar talakawa wajen biyan matarsa da 'ya'yansa albashi a kan aikin da basu yi ba.
Tuhumar dai ta kara dakushe damar tsohon Firaministan na samun nasara a zaben shugaban kasar da za'a gudanar a Faransar a ranakun 23 ga watan Aprilu da kuma 7 ga watan Mayu wanda ake hasashen zai kasance a kan gaba.
A ranar talatar nan ce dai alkalai masu gabatar da kara suka gabatar da tuhumar ga Francois Fillion a hukumance.
Sai dai kuma Fillion wanda yace bai aikata wani laifi ba, ya ci alwashin cigaba da yakin neman zabe.