An gabatar da takardun Karar Jacob Zuma | Labarai | DW | 28.12.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An gabatar da takardun Karar Jacob Zuma

Masu shigar da kara a madadin gwamnatin afrika ta kudu ,sun gabatar wa sabon shugaban jamiiyyar ANC Jacob Zuma takardun gayyatar sa zuwa gaban ,dangane da zargin da ake masa na cin hanci.Lauyoyin Zuma sun bayyana cewar an gabatar da wadannan takardu ne a gidansa dake Johanesburgh alokacin da baya nan.Hukumomar shigar da karrarkin Afrika ta kudun dai na gudanar da bincike dangane da zargin shugaban na ANC da akeyi da laifin karban cin hanci da rashawa a wasu harkoki da suka danganci cinikin makamai.A watan daya gabata nedai Zuma ya doke shugaba Thabo Mbeki a zaben shugaban cin jamiiyyar ANC da akayi.A watan Augustan shekara mai kamawa nedai ake saran fara sauraron wannan sharia.