An gabatar da rahoton Timor Ta Gabas | Labarai | DW | 21.01.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An gabatar da rahoton Timor Ta Gabas

Shugaban yankin Timor ta Gabas Xanana Gusmo ya mikawa babban sakataren MDD Kofi Annan rahoton karshe game da keta ´yancin ´yan Adam a lokacin mulkin Indonesia a yankin. A cikin rahoton, hukumar tsage gaskiya da sansatawa ta tabbatar cewar akalla mutane dubu 102 da dari 800 aka halaka ko kuma suka bace a yankin daga shekarar 1974 zuwa 1999. Wannan adadin ya yi daidai da kashi 10 cikin 100 na ilahirin al´umar yankin Timor ta Gabas. Gusmo ya ce ba manufar kasar sa ce daukar fansa ba, a´a illa kawai adalci take son a nuna. Shugaban ya ce kamar a ATK, dole ne a koyi darasi daga wannan ta´asa don hana sake aukuwar ta a gaba.