1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An gabatar da kundin yarjejeniyar gwamnatin kawance ta Jamus

Mohammad Nasiru AwalNovember 12, 2005

Dukkan wakilan jam´iyun SPD da CDU da kuma CSU sun nuna gamsuwa da ka´aidojin yarjejeniyar

https://p.dw.com/p/Bu4F
Shugabannin manyan jam´iyun 3 a taron manema labarai
Shugabannin manyan jam´iyun 3 a taron manema labaraiHoto: AP

An kasance cikin hali na farin ciki lokacin da wakilan sabuwar gwamnatin kawance ta tarayyar Jamus suka gabatar da kundin yarjejeniyar mai shafuka kusan 200 yau a birnin Berlin, ko da ya ke ala tilas sassan biyu suka amince da wasu ka´idojin yarjejeniyar, kamar yadda shugaban SPD mai jiran gado Matthias Platzeck ya nunar:

“Abin da muka amince da shi a nan dai ba auren soyayya ba ne, a´a wani mataki ne da ya dace kuma ya zama wajibi mu dauka.”

To sai dai wannan matakin mai fai´da ne ga Jamus inji shugabar CDU kuma shugabar gwamnati mai jiran gado Angela Merkel.

“Jamus na cikin wani hali na tsaka mai wuya, amma burin mu shi ne mu yi amfani da wannan dama ta kawance manyan jam´iyun don fid da ita daga cikin wannan kangi na wahalhalu.”

Al´umar kasar ta Jamus dai na fatan wannan babban kawance zai iya magance manyan matsaloli kuma masu daure kai da kasar ke fuskanta musamman dangane da gibin kasafin kudi na kimanin Euro miliyan dubu 35 da kuma dinbim bashin dake kan gwamnatin tarayya.

Babban aikin dake gaban wannan gwamnatin kawance wadda ta kasance mafi girma a Jamus cikin shekaru 40, shine aiwatar da canje-canje da kara daukar matakan yin tsimin kudi. A farkon shekara ta 2006 za´a share fagen samar da bunkasar tattalin arziki sannan daga shekara ta 2007 shirin tsimin kudin zai kankama.

Alal misali daga watan janerun shekara mai zuwa za´a kara yawan kudin harajin kayan alatu daga kashi 16 zuwa 19 cikin 100 sannan a kara harajin ma´aikata masu albashi mai tsoka daga kashi 42 zuwa 45 cikin 100 a wani mataki na dakile gibin kasafin kudi. Burin gwamnatin tarayya dai shi ne ta cike ka´idojin yarjejeniyar Maastricht daga shekara ta 2007. Baya ga cike gibin kasafin kudi wani muhimmin abu dake gaban gwamnati kamar yadda Angela Merkel ta nunar shine samar da sabbin guraben aikin yi a cikin kasar. Hakan kuwa shi zai zama wani sikelin auna nasarar da gwamnatin kawance zata samu. Merkel na mai fatan cewa nan da shekaru 10 masu zuwa Jamus zata koma matsayin ta na daya daga cikin kasashen Turai 3 mafi karancin marasa aikin yi.

To sai dai ´yan adawa musamman jam´iyun The Greens da kuma FDP da manyan kamfanonin kasar sun zargi sabuwar gwamnatin kawance da rashin gabatar da sahihan matakan da za su kai kasar tudun mun tsira.

To amma shugaban SPD mai barin gado Franz Müntefering ya yi watsi da wannan zargi yana mai cewa:

“Duk mai yiwa kasar nan fatan alheri to dole ya ba mu damar aiwatar da wadannan canje canje duk da cewa jama´a zasu ji radadinsa a jika.”

Bayan makonni da dama suna shawarwari dukkan jam´iyun SPD, CDU da kuma CSU sun yi kyakkyawan fatan cewa gwamnatin kawance ce kafa daya tilo da zata iya magance matsalolin da kasar ta Jamus ke fuskanta.