An gabatad da rahto kan haramtattun ayyukan CIA a nahiyar Turai. | Siyasa | DW | 08.06.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

An gabatad da rahto kan haramtattun ayyukan CIA a nahiyar Turai.

Kwamitin nan da Majalisar Masahawarta ta Tarayyar Turai ta kafa don ya binciki zargin da ake yi wa ƙungiyar leƙen asirin Amirka, wato CIA, na cafke da kuma jigilar fursunoni ba bisa ƙa'ida ba, zuwa wasu sansanoninsu na sirri a wasu kasashen Turai don yi musu tambayoyi, ya gabatad da rahotonsa.

Dick Marty, yayin da yake gabatad da sakamakon da bincikensa.

Dick Marty, yayin da yake gabatad da sakamakon da bincikensa.

Shugaban kwamitin da Majalisar Mashawarta ta Tarayyar Turai ta kafa, don binciken sansanonin sirrin nan a nahiyar Turai da ake zargin ƙungiyar leƙen asirin CIA da kafawa, Dick Marty, ya gabatar da sakamakon aikin da suka yi, inda ya ce ƙasashe da dama na nahiyar Turai sun mara wa kungiyar leƙen asirin CIA baya, wajen yin jigilar fursunonin da aka cafke su ba bisa ƙa’ida ba. A cikin rahoton da kwamitinsa ya buga, Dick Marty, ya bayyana cewa jami’an leƙen asirin Amirka, sun sace mutanen da suke tuhumarsu inda kuma suka yi jigilarsu zuwa sansanonin sirrin da suka kafa a yankuna da dama na Turan:-

„Mun tabbatar a yau, fiye da kullum, cewa wannan shiri ba zai taɓa yiwuwa ba tare da tallafin da wasu ƙasashe suka bayar ba.“

Rahoton dai ya zargi Jamus ne da rashin kulawa ko kuma nuna sassauci da rufe ido kan jigilar fursunonin da aka yi ta yi daga harabarta. Dick Marty ya ambaci filin jirgin saman soji na Ramstein da ke jihar Rheinland-Pfalz a nan Jamus, inda daga nan ne aka fi yin yawan jigilar. Ƙasashen Turkiyya da Spain da Cyprus da Azerbajan na cikin waɗanda rahoton ya yi wa zargi da tallafa wa kungiyar ta CIA, a wannan ɗaukin.

A zahiri dai, inji Marty, Jamus ta take hakkin wasu mutane da ƙungiyar leƙen asirin ta cafke su, kamarsu Khaled al Masri, mai fasfot ɗin Jamus, wanda aka cafke daga Macedoniya zuwa Afghanistan da kuma ɗan ƙasar Masar nan da aka kame a Italiya, sa’annan daga baya aka yi jigilarsa zuwa Masar. A taƙaice dai, ƙungiyar leƙen asirin Jamus ta sami labarin cafke el Masri da aka yi a Macedoniya.

Dick Marty ɗin dai ya zargi mahukuntan Macidoniyan ne da ƙin ba shi haɗin kai a lokacin gudanad da binciken kwamitin. Gaba ɗaya dai rahoton ya ce ƙasashe 14 na Turai ne ke da hannu a ɗaukin na ƙubngiyar CIA, wadda ke da sansanoni a yankuna daban-daban na duniya, inda ake gallaza wa fursunoni wajen yi musu tambayoyi. Kwamitin dai ya ce ya gano wani shiri na zirga-zirgan jiragen saman ƙungiyar CIA ɗin, daga Turai zuwa Guantanamo Bay, amma tare da bi ta Iraqi da kuma Afghanistan. A Palma de Mallorca na Spain ne dai ƙungiyar ke da cibiyar wannan zirga-zirgar.

Dick Marty dai ya fi zargin Romaniya da Poland, inda ya ce ya sami sabbin hujjojin da ke tabbatad da cewa, a waɗannan ƙasashen, an tsare mutane da dama da aka kame su ba bisa ƙa’ida ba, inda kuma aka yi ta musu tambayoyi, ko kuma har ila yau ma ake ci gaba da wannan salon. A kasar Poland dai, ana kai fursunonin ne a gidan yarin Szymany, sa’annan a Romaniya kuma, ana kai su gidajen yarin Bukarest ne ko kuma Timisoara. Akwai dai alamu da yawa da ke nuna cewa, da akwai sansanonin CIAn da dama a Turai.

Tuni dai, ƙasashen Romaniya da Poland da gwamnatin Amirka sun yi watsi da zargin.

Duk da gabatar da wannan rahoton dai, Dick Marty, ya ce ba ƙarshen aikinsu ba ke nan. Kamar yadda ya bayyanar:-

„Na yi imanin cewa, da akwai bukatar da ta taso, wadda ke neman tabbatad da gaskiya. A ko yaushe muna ta kara samun hujjoji da kuma mutane ɗai-ɗai, waɗanda ke bayyana shirinsu na ƙara ba mu haske.“

A ran 27 ga wannan watan ne dai, Hukumar Ƙungiyar Tarayyar Turan, za ta fara nazarin rahoton, bayan Majalisar Mashawarta ta rattaba kansa a wannan ranar. Kwamishinan shari’a na Ƙungiyar EUn, Franco Frattini, ya yi barazanar ɗaukaka ƙara ko kuma sanya takunkumi kan duk ƙasashe mambobin ƙungiyar, waɗanda aka same da hannu a haramtattun ayyukan da ƙungiyar leƙen asirin CIA ɗin ta gudanar.

 • Kwanan wata 08.06.2006
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Btzn
 • Kwanan wata 08.06.2006
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Btzn