1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An ga alamun komayawa zagayen taron Doha kan cinikaiya

January 27, 2007
https://p.dw.com/p/BuT9

Bisa ga dukkan alamu nan ba da dadewa ba za´a koma wani zagaye na shawarwarin Doha game da sakarwa harkokin kasuwancin a duniya mara. An ga haka ne a gun taron tattalin arzikin duniya dake gudana a garin Davos na kasar Switzerland. Rahotanni sun nunar da cewa wakilan ministocin cinikaiya na kasashe 30 daga cikin membobi 150 na kungiyar ciniki ta duniya WTO, sun amince da wata shawara game da komawa ga tattaunawar da shugaban kungiyar WTO Pascal Lamy ya gabatar. A cikin watan yulin shekara ta 2006 aka tashi baram baram a taron na Doha, saboda Amirka da KTT sun ki su rage yawan kudaden tallafi da suke bawa manoman su. Manufar taron na Doha wanda aka fara a shekara ta 2001 ita ce kulla wata yarjejeniya da zjmar kawad da dukkan shingayen cinikaiya musamman ga kayaki daga kasashe masu tasowa.