1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An fuskanci tashe tashen hankula a Iraq

November 3, 2005
https://p.dw.com/p/BvMc

A yau alhamis jamian yan sanda na iraqi sun rasa rayukan su sakamakon musayar wuta data wanzu a tsakanin su da yan fadan sari ka noke.

Bugu da kari bayanai daga kasar ta iraqi sun shaidar da rahoton fuskantar wasu yan tashe tashen hankula a yankin mabiya darikar sunni. Hakan kuwa yazo ne a dai dai lokacin da musulman kasar suka fara hutun kwanaki uku na babbar sallah, bayan kammala azumin watan ramalana.

A waje daya kuma jamian yan sanda na kasar sun shaidar da cewa an gano gawarwakin mutanen nan goma sha biyu da akace anyi garkuwa dasu.