1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An fuskanci sabon tashin hankali a Somaliya

Halimatu AbbasJuly 26, 2010

Mutane 8 sun mutu a cikin wata arangama a Somaliya.

https://p.dw.com/p/OUOL
Mutane ɗauke da wani da ya samu rauni a wani hari da aka ƙaddamar a Mogadishu.Hoto: AP

Wani jami'in gwamnatin Somaliya ya sanar da cewar, taho mu gama a tsakanin dakarun gwamnatin Somaliya da kuma masu ta da ƙayar baya a birnin Mogadishu, ya yi sanadiyar mutuwar aƙalla mutane 8, a yayin da wasu 17 kuma suka sami rauni. Shugaban sashen kula da masu ɗaukar marasa lafiya a birnin Mogadishu, fadar gwamnatin Somaliya, Ali Muse ya ce a yammacin Asabar ce mutane biyar suka mutu, kana da safiyar Lahadin nan kuma wasu mutane ukku suka bi sahu, a yayin da wani makamin roka ya faɗa a tsakiyar wata kasuwa. A cewar Ali Muse galibin mamatan fararen hula ne.

Wannan labarin ya zo ne a daidai lokacin da taron ƙoli na shugabannin ƙasashen Ƙungiyar Tarayyar Afirka(AU) da ke gudana a birnin Kampla na ƙasar Yuganda, ke tattauna batun Somaliya. Taron yana mayar da hankali ne akan matsalar Somaliya bayan da wasu mutane 76 suka mutu sakamakon tagawayen hare-haren bama-bamai - kimanin makonni biyu a ƙasar ta Yuganda. Mayaƙan ƙungiyar al-Shabab, wadda cibiyarta ke Somaliya ne ta ɗauki alhakin ƙaddamar da hare - haren. Masu ta da ƙayar baya dai na fafutuka ne domin kifar da gwamnatin Somaliyar da ke samun goyon bayan Majalisar Ɗinkin Duniya da kuma ƙasashen yammaci, musamman a shekaru ukun da suka gabata.

Mawallafi: Saleh Umar Saleh

Edita: Halima Balaraba Abbas