An fara zaben gwamnoni a jihohin Nigeria | Labarai | DW | 14.04.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An fara zaben gwamnoni a jihohin Nigeria

Hukumomin tsaro a tarayyar Nigeria na cikin shirin kota kwana adangane da zaben da aka fara a wannan kasa mai mafi yawan alummomi a nahiyar Afrika.Ayau dai alummomin Nigerian na gudanar da zaben gwmnonin jihohi ne ,da wakilan majalisar dokoki,gabannin zaben shugaban kasa dana yan majalisar tarayya a ranar asabar mai zuwa.A yankin kudancin kasar dai ,yan bindiga dadi sun kai farmaki wani ofishin yansanda,inda suka kashe jamian tsaron guda 7 a cikin birnin Porthacourt.Yansanda sun sanar dacewa an kuma kashe wasu jamian siyasa guda uku.Tuni dai shugaba Obasanjo yayi gargadin daukan matakan tsaro dangane da dukkan wadanda suka nemi tayar da hankali lokacin zaben.