An fara yiwa Mullah Obaidullah tambayoyi a birnin Islamabad | Labarai | DW | 03.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An fara yiwa Mullah Obaidullah tambayoyi a birnin Islamabad

Jami´an Pakistan da na Amirka sun fara yiwa tsohon ministan tsaron gwamnatin Pakistan tambayoyi a birnin Islamabad. Rahotanni sun nunar da cewa a ranar laraba da ta gabata aka kame Mullah Obaidullah Akhund tare da wasu mutane 4 a birnin Quetta dake kudu maso yammacin Pakistan. Ana daukar Akhund a matsayin wani kusa a cikin kungiyar Taliban kuma jami´ai na fatan zai taimaka a gano sauran shugabannin sojojin sa kai na Taliban. To sai dai har yanzu gwamnatin Pakistan ta ki ta tabbatar da kamun sa, wanda kungiyar Taliban ta musanta. A kuma can kasar Afghanistan akalla mutane biyu sun rasu sannan 16 sun jikata a wani harin bam da aka kai a lardin Herat.