1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An fara wani zagaye na tattaunawa tsakanin Solana da Larijani

June 23, 2007
https://p.dw.com/p/BuI2

Babban jami´in diplomasiyar KTT Javier Solana ya ce yana da kyakkyawan fata a tattaunawar da suka fara yau akan shirin nukiliyar Iran. To sai dai ya ce ba ya tsammani za´a cimma wani gagarumin sakamako. Solana ya nunar da haka ne a gaban manema labarai gabanin ya shiga tattaunawa da babban mai shiga tsakani na Iran akan shirinta na nukiliya Ali Larijani a birnin Lisbon na kasar Portugal. A jiya juma an jiyo shugaban hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa IAEA, wato Mohammed El-Baradei na cewa Iran ta nuna shirin komawa kan teburin shawarwari da hukumarsa.

O-Ton Baradei:

“Ina fatan cewa zamu koma kan teburin shawarwari a cikin ´yan makonni masu zuwa. Muna tsara wani shiri wanda nake fata zamu kammala shi a cikin watanni biyu. Larijani da kan shi yayi mana alkawarin cewa Iran zata yi aiki da mu don warware dukkan batutuwan da suka saura.”