An fara tuhumar wasu yan ta´adda a Biritaniya | Labarai | DW | 09.05.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An fara tuhumar wasu yan ta´adda a Biritaniya

Jami´an yan sanda a Biritaniya sun cafke wasu mutane hudu da ake zargi yan ta´adda ne. Daga cikin mutanen a cewar bayanai, akwai madugun yan kunar bakin waken nan da suka tashi wasu bama bamai a birnin London a watan yuli na shekara ta 2005.

An dai cafke mutane hudun ne bisa zargi da ake musu da shiryawa da kuma kokarin kai hare hare na ta´addanci ne, a cikin kasar ta Biritaniya.

An dai cagfke mutane hudun ne a sanadiyyar wani sintiri da jami´an yan sandan suka gudanar ne a safiyar yau a , garuruwan Yorshire da Midlands ne.

Tuni dai akayi awon gaba da mutanen izuwa ofishin yan sanda dake London, don amsa tambayoyi, dake da nasaba da tashin bama baman nan na birnin London da yayi ajalin mutane da daman gaske.