An fara tattaunawa tsakanin tawagar MDD da gwamnatin Isra´ila | Labarai | DW | 18.07.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An fara tattaunawa tsakanin tawagar MDD da gwamnatin Isra´ila

Wata tawagar MDD ta fara tattaunawa da gwamnatin Isra´ila a game da mummunan halin da ake ciki a yankin GTT. Manzon MDD Terje Roed-Larsen ya bayyana tattaunawar da suka yi yau da safe da ministar harkokin wajen Isra´ila Zippi Livni a birnin Kudus da cewa ta yi armashi. Mista Larsen ya ce an gabatarwa Isra´ila da kuma Libanon jerin shawarwari wanda yanzu haka suke nazari akansu. Yace dukkan sassan biyu sun amince cewa da akwai bukatar samar da wani kwakkwarar shirin tsagaita bude wuta. Larsen ya ce sun amince zasu ci-gaba da shawarwarin a Isra´ila da kuma a Libanon a cikin kwanakin nan masu zuwa. A lokacin da take magana a taron manema labarai bayan tattaunawar ministar harkokin wajen Isra´ila Zippi Livni cewa ta yi gwamnatin Libanon ta nunar da cewa ba ta da karfin sojin da zata iya daidaita al´amura a cikin kasarta.