An fara tattaunawa tsakanin Amirka da China
May 24, 2010Sakatariyar harkokin wajen Amirka Hillary Clinton ta isa China domin tattauna hanyoyin cigaban kasuwanci da kuma magance matsalar tattalin arziki dake addabar duniya.
A jawabin sa wajen wani taro na haɗin guiwa Firaminista Hu Jintao yayi alƙawarin gudanar da sauye-sauye dake daya shafi darajar kuɗin ƙasar na Yean, amma kuma a bisa tsarin da ƙasar ta Sin zata amince dashi. A lokacin wannan ziyara, Hillary Clinton ta isa Beijing da tawagar 'yan kasuwa da jami'an gwamnati kimanin 200.
Clinton tayi amfani da ziyarar ta wajen taɓo matsalar nitsar da jirgin ruwan Koriya ta Kudu da ake zargin Koriya ta Arewa da aikatawa: tace yau muna fuskantar wani gagarumar kalubale daya biyo bayan nitsar da jirgin ruwan koriya ta kudu saboda haka akwai buƙatar aiki tare domin fuskantar ƙalubalen dake gaban mu na tabbatar da zaman lafiya a yankin tsibirin ƙasashen Koriya.
Mawallafi: Babangida Jibril
Edita: Yahouza Sadissou Madobi