An fara taron kolin hukumar IAEA a Vienna | Siyasa | DW | 06.03.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

An fara taron kolin hukumar IAEA a Vienna

Kasar Iran ta kara yin wani sabon kurarin

Shugaban kasar Iran, Ahmadinajad

Shugaban kasar Iran, Ahmadinajad

Ya zuwa yanzu dai, a yayin da gwamnonin zartarwa na hukumar kula da makamashin nukiliya ta Mdd 35 suka fara taron kolin su a birnin Vienna, a game da matakin da kasar Iran take kokarin dauka na kera makamin Atom, a dai dai lokacin ne kuma mahukuntan Iran suka kara yin kurarin ci gaba da aiwatar da matakin da suka dauka tun da farkon fari.

A dazu dazun nan ne dai mahukuntan na Iran suka yi kurarin ci gaba da sarrafa sanadarin na su na Uranium, amma a wannan lokaci da gasken gaske matukar hukumar ta IAEA ta ci gaba da daukar matakan kai karar kasar a gaban kwamitin sulhu na Mdd, a lokacin taron hukumar da aka fara a yau.

Kafin dai fara wannan taro, kasar Amurka tuni tayi nisa wajen janyo hankalin mambobin wannan hukuma da su dauki matakin mika kasar ta Iran a gaban Mdd, don ladaftar da ita, ta hanyar sakala mata takunkumi.´

Kokarin daukar wannan mataki daga bangaren mahukuntan na Amurka da kuma kawayen nata ya biyo bayan zargi ne da suke wa kasar ta Iran da kokarin kera makamin na aton ,wanda suka ce zai zamo barazana ga zaman lafiya ne a duniya baki daya.

A waje daya kuma jakadan kasar Amurka a Mdd, Wato John Bolton cewa yayi kamata yayi a wannan lokaci hukumar ta IAEA ta dauki tsattsauran mataki akan kasar ta Iran, don dakile wannan mummunan aniyar tata.

Ita kuwa kasar India wacce ta dade tana da kyakkyawar alaka da kasar ta Iran , cewa tayi kamata yayi a dauki matakan sulhu don warware wannan takaddama, ba tare da an kai ruwa rana ba.

Ya zuwa yanzu dai duk da wannan matsayi da ake ciki, shugaban hukumar ta IAEA, wato Mohd El Baradei cewa yayi har yanzu yana da fatan cewa za´a samo bakin zaren warware wannan rigima daga yanzu izuwa karshen makon gobe.

Wannan bayani dai na El baradei yazo ne jim kadan kafin fara taron kolin hukumar ta IAEA a yau din nan a can birnin Vienna.

Rahotanni dai sun nunar da cewa a lokacin wannan taro ana sa ran cewa wakilan hukumar zasu zartar da hukuncin kai karar kasar ta Iran a gaban kwamitin sulhu na Mdd, cewa kasar ta Iran ta gaza yin cikakken bayani da za´a gamsu dashi a game da wannan shiri da ake zargin ta da kokarin aiwatarwa.

A watan fabarairun daya gabata ne Mdd ta dakatar da daukar wani kwakkwaran mataki akan kasar ta Iran , har sai ta samu cikakken rahoto daga hukumar ta IAEA, bayan kammala wannan taro data fara a yau.

Daga dai tun lokacin da aka fara wannan kace nace izuwa yanzu, kasar ta Iran tace nukiliyar da take kokarin kerawa na zaman lafiya ne amma ba na tashin hankali ba kamar yadda ake zato a can baya.

 • Kwanan wata 06.03.2006
 • Mawallafi Ibrahim Sani
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu1J
 • Kwanan wata 06.03.2006
 • Mawallafi Ibrahim Sani
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bu1J