1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An fara shari'ar wasu 'yan Boko Haram a Nijar

A Jamhuriyar Nijar babban alkalin alkalai na kasar ya ba da sanarwar cewar an fara yi wa wasu gomai na dubban jama'a na Kungiyar Boko Haram da ma masu mara musu baya shari'a tun a farkon wannan wata na Maris a asirce.

Alkalin alkalan Chaibou Samna ya ce mutanen wadanda ake yi wa shari'ar sun hada da 'yan kasashen Nijar da Najeria da kuma Mali, wanda kuma ya ce za a kwashe wata da watanni ana yi musu shari'a. Wadanda yawanci daga cikin wadanda ake zargin da laifin ayyukan ta'addanci za su iya fuskantar hukuncin dauri na shekaru goma zuwa 20 a gidan kurkuku.