An fara samun sakamakon zabe a Nigeria | Labarai | DW | 15.04.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An fara samun sakamakon zabe a Nigeria

A Nigeria an fara samun sakamakon zaben gwamnonin jihohi dana yan majalisun dokoki da aka gudanar a kasar a jiya. Rahotanni daga sassan Nigeriar na nuni da cewa tarzoma da harkalla ta magudi da Almundahana sun dabaibaye shaánin zaben a mafi yawancin jihohi. An fuskanci matsaloli masu yawa musaman a yankin Niger Delta mai arzikin mai dake kudancin kasar inda a kalla mutane goma sha bakwai suka rasa rayukan su. A jihohin Anambara da Delta, matasa wadanda suka fusata da rashin aikewa da katinan zabe a mazabu sun afkawa ofishin hukumar zaben domin nuna bacin ran su. Can kuwa a garin Port Harcourt dake jihar Rivers yan sanda bakwai da fararen hula uku suka rasa rayukan su bayan da wasu yan takife suka bankawa ofishin yan sandan wuta. Duk da matsalolin da aka fuskanta shugaban hukumar zaben mai zaman kanta Moris Iwu yace ya gamsu da yadda zaben ya gudana. Shima dai a nasa bangaren shugaban Nigeria Olusegun Obasanjo yace yace yayi Amanna sakamakon zaben zai kasance sahihi kuma karbabbe ga jamaá.