1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An fara samun sakamakon zaɓe a ƙasar Uganda

February 24, 2006
https://p.dw.com/p/Bv6r

Sakamakon farko na zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar a ƙasar Uganda ya nuna shugaban ƙasar Yoweri Museveni shi ne a kan gaba a bisa abokin hamaiyar sa kizza Begiye. Sai dai kuma ana samun sabani a rahotannin da kafofin yada labarai na cikin gida suke bayarwa wanda ya nuna an takarar na kunnen doki. A sakamakon da hukumar zaɓen ta sanar Yoweri Museveni na da kashi 59.5 cikin ɗari na ƙuriún da aka ƙidaya yayin da babban mai ƙalubalantar sa kuma madugun jamíyar adawa Kizza Besigye ya sami kashi 37.2 na adadin ƙuriún. Wajibi ne ɗan takara ya sami kashi hamsin cikin ɗari na yawan ƙuriún domin samun galaba. Idan kuma baá sami ɗan takarar da ya sami wannan adadi ba, zaá kai ga sake karawa a zagaye na biyu na zaɓen. Ya zuwa yanzu dai hukumar zaɓen ta baiyana cewa ta ƙidaya adadin ƙuriú 526,000. Mutane miliyan 10.4 ne suka yi rejistar kaɗa ƙuriá sai dai bayanai sun nuna cewa kashi 62 ne kawai cikin ɗari suka kaɗa ƙuriár su.