An fara kirga kuri′u a zaben Afghanistan | Siyasa | DW | 20.09.2005
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

An fara kirga kuri'u a zaben Afghanistan

A yau ne ake kirga kuriu a zaben kasar Afghanistan karo na farko bayan kusan shekaru talatin

zabe a Afghanistan

zabe a Afghanistan

A fara kirga kuriun ne a cobiyoyin kirga kuriu a Herat,Bamiyan,Kunduz,Kandahar,kodayake akwai yiwuwar samun jinkiri a lardin Nangarhar dake gabashin kasar inda aka samu matsalar dauko kuriu daga larduna biyu zuwa cibiyoyin kirga su.

An dai yi anfani da Jakkai,rakuma dawaki da jirage masu saukar angulu wajen daukar akwatunan zabe daga yankunan Hamada na kudancin kasar da kuma yankuna masu tsaunuka dake arewacin kasar zuwa wuraren kirga kuriun na daya daga cikin zabuka masu tarihi da Mjalaisar Dinkin Duniya ta taba shiryawa.

Kimanin masu jefa kuria miliyan shida ne cikin mutane miliyan 12 da aka yiwa rajista suka kada kuriar tasu a zaben majalisar dokoki da kananan hukumomi a zagaye na karshe na shirye shiryen kasashen duniya domin wanzar da demoktradiya a kasar Afghanistan bayan fatatakar yan Taliban na kasar Amurka tayi daga mulkin kasar a 2001.

Wani mai Magana da yawun hukumar zabe Aleem Siddique yace zuwa ranar alhamis ake sa ran kamala kaiwa akwatunan zaben zuwa cibioyin haka kuma mutane 7000 ake sa ran zasu yi aiyukan kiga kuriun.

Ana sa ran cewa zaa dauki kwanaki 16 ana krga kuriun wanda ake sa ran samun sakamakonsa ranar 22 ga watan oktoba mai zuwa.

Kasashe kawayen Afghanistan sun yabawa wannan zabe ,amma masu nazari sun baiyana cewa zaa samu matsala wajen gudanar da harkokin majalisar saboda mafi yawa nay an takara suna harkokinsu ne a matsayin masu zaman kansu maimakon karkashin inuwar wata jamiya.

Kuma ganin cewa zasu fi maida hankali ne akan harkokin yankunansu maimakon wadanda suka shafi kasar baki daya masu lura na ganin cewa hakan zai kawo cikas ne maimakon taimakawa kokarin Karzai na tabbatar karfin gwamnatin taraiyar kasar.

Kungiyar Taliban dai tayi kira ga jamaa da su kauracewa zaben amma kuma bata samu nasasar lalata shirye shiryen zaben ba duk kuwa da tashe tashen hankula da ta haddasa da suka yi sanadiyar mutuwar mutane kusan 1000.

Akalla kuma mutane 14 suka rasa rayukansu a karshen mako amma duk da haka zaben ya tafi lami lafiya a yawancin yankunan.

Cikin wani hoton bidiyo da gidan TV na aljazeera ya nuna jiya litinin mataimakin Osama bin laden Ayman al zawari yana cewa zaben na bogi ne kuma an gudanar da shi ne karkashin mamayar Amurka.

Yace har yanzu kungiyar Taliban tana nan da karfinta kuma ya gargadi dakarun Amurka da su boya cikin sansanonisu.

Tawagar sa ido ta KTT a zaben na Afghanistan tace zaben ya gudana cikin lumana kuma wani muhimmin mataki ne ga kokarin kasar na komawa tafarkin demokradiya.

Jakadan Amurka Ronald Neumann yace wannan zabe ba wai ya kawo karshen taimakon kasashen duniya ga Afghanistan bane, yace a halin yanzu kasashen sun fara wani shiri na kara taimakawa kasar.

A halin da ake ciki kuma a safiyar yau din nan ne aka harba roket a birnin Jalalabad inda mutum guda ya samu rauni kamar dai yadda kakakin maaikatar cikin gida Yusuf Stanikazai ya baiyanawa manema labarai.

 • Kwanan wata 20.09.2005
 • Mawallafi Hauwa Abubakar Ajeje
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvZW
 • Kwanan wata 20.09.2005
 • Mawallafi Hauwa Abubakar Ajeje
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvZW