An fara kidayar jamaar Najeriya | Labarai | DW | 21.03.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An fara kidayar jamaar Najeriya

NIGERIA

Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo,ya tabbatar sadaukar da kann gwamnatinsa ga samun nasasar kidayar jamaa da gidaje da ake farawa yau a kasar,yana mai bada tabbacin cewa ba wani ajanda na boye tattare da wannan kidaya.

Cikin jawabi da yayiwa kasa ta gidajen rediyo da telebijin game da kidayar jamaa ta 2006,shugaban na Najeriya yace wannan kidaya bata da alaka da siyasa,saboda haka kada a dauke ta tamkar wata gasa ce ta nuna karfi ko yawa.

Akalla mutane 6 suka rasa rayukansu a rikice rikice da ke da alaka da wannan kidaya a jihar Ondo dake kudu maso yammacin kasar,yayinda aka samu wasu tashe tashen hankula a wasu yankuna na arewa.

Obasanjo ya yabawa abokan ci gaba na kasar,musamman kungiyar taraiyat turai wadda ta bada gudumowar dala miliyan 150 domin gudanar da wannan kidaya.

A kidaya na baya a 1991 ya nuna cewa jamaar Najeriya su miliyam 88 da dabu 900,amma adadin da Majalisar Dinkin Duniya dana gwamnati suka bayar na baya ya nuna cewa jamaar Najeriya sun kai tsakanin miliyan 120 zuwa 150.