An fara kampe a kasar Chadi | Siyasa | DW | 24.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

An fara kampe a kasar Chadi

Shugaban Chadi, Idriss Deby Itno ya lashi takobin tauye hakkin yan adawa dake neman hana shi yin Tazarce a zabe na gaba.

A kasar Chadi al'amura na kara tabarbarewa a daidai lokacin da aka shirya gudanar da zaben shugaban kasa wanda shugaba Idriss Deby Itno da ke kan karagar mulki kusan shekaru 26 zai sake tsayawa takara a wa'adi na biyar. Yanzu haka yan sanda a kasar na tsare da wasu mutane guda hudu koma fiye da haka, wakilai na kungiyoyi masu fafutuka wadanda suka kira da a yi zanga-zanga domin nuna adawa da tazarcen na shugaba Deby.

Mutum na farko da 'yan sandar suka cafke shine Mahamat Nour Ahmed Ibedou, shugaban hadin gwiwar wasu kungiyoyi masu fafutuka da ake kira da sunan Ca suffit, watau ya isa, wanda aka kama a ranar Litinin din nan. Kana a ranar Talata aka tsare Younouss Mahadjir, mataimakin shugaban kungiyar kwadago ta kasar watau UST da kuma Nadjo Kalina Palmer kakakin kungiyar Iyinat, mai taken mun gaji. Maitre Kamneloum Djirabie Delphine ita ce lauyar da ke karesu.

"Ta ce wannan gangami da wakilai na kungiyoyin farar hula suka kira ba shi ba ne na farko, akwai yajin aikin gama garin da aka yi da sauran bore domin nuna adawa da takarar ta Idrss Deby, wadanda hanyoyi ne na lumana da kungiyoyin fara hula suke bi. Ba su kauce daga hanya ba don haka babu wata hujja ta tsaresu."

Straßenszene Ndjamena

Birnin Ndjamena

A makon jiya ne dai kungiyoyin farar hula suka yi kira ga al ummar kasar ta Chadi a duk fadin kasar da su gudanar da gangamin da kuma jerin gwano don nuna damuwarsu a kan takarar ta Idriss Deby a zaben na 10 ga watan Afrilu. To sai dai ministan cikin gida na kasar Ahamat Mahamat Bashir ya haramta zanga-zangar. Barka Michel, shugaban hadin gwiwar kungiyoyi na kasar ta Chadi ya ce an shiga wani hali na takurawa jama'a.

"Ya ce Allah-kulli halin, babu gudu babu ja da baya, sai abinda hali ya yi kuma muna kira ga magoya bayanmu da al ummar kasar da suka kara zage damtse, dangane da abinda ake son a yi. Ba fa za mu rufe bakinmu ba a kan wadannan bukatu da muka gabatar."

Tun da farko lokacin da aka kaddamar da yakin neman zabe na kasar, shugaba Deby ya yi hannunka-mai-sanda ga duk wadanda suka kudiri aniyar kawo mashi tarnaki a game da burinsa na ci gaba da mulkin sai mahadi ka ture. A cikin wata sanarwa da ta bayyana, kungiyar Amnesty Internatioonal ta yi alllah wadai da kame-kamen, sannan ta bukaci gwamnatin Chadin da ta saki mutanen.

Ahmet Malum na daya daga cikin wakilai na kungiyoyin kare hakin jama'a na Chadin.

"Ya ce ba za mu yi kasa a giwa ba idan suna tsamanin rufe jami'an kungiyoyin ma su fafutuka wata dama ce ta cin nasara a zaben, ba haka abin yake ba kundin tsarin mulki na kasar Chadi ya ba mu yancin yin zanga zanga.

Kasar ta Chadi dake a yankin tsakiyar Afrika na daga cikin kasashen A da suka fi fama da talauci duk da arzikin man fetir din da ta mallaka saboda abinda wasu jama'ar kasar suka kira rashin iya gudanar da mulki na shugabanninta.

Sauti da bidiyo akan labarin