1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An fara kama hanyar Mulkin Dimokradiyya a Mauritania

November 29, 2005
https://p.dw.com/p/BvIp

Shugaban mulkin soji na wucin gadi a kasar Mauritania, wato Ely Ould Mohd ya rantsar da jamian hukumar zabe na kasar mai zaman kanta goma sha biyar a yau talata.

Wannan rantsuwa dai na a matsayin kafa ne da zata bude sabon babi na kara kaimi game da kokarin da ake na gudanar da zabe a kasar.

Jim kadan bayan rantsar da jamian hukumar, Ould Mohd ya tabbatar musu da goyon bayan gwamnatin sa don sauke nauyin da aka rataya musu na shirya zabe da kuma gudanar dashi bisa gaskiya da adalci.

Duk da cewa wannan gwamnati ta Ely Ould Mohd ta samo asali ne da karfin tuwo, tuni ta dade da samun goyon bayan da yawa daga cikin yan kasar a hannu daya kuma da kasashen duniya.

Rahotanni dai sun shaidar da cewa wannan gwamnati ta dare madafun ikon kasar ne bayan data kifar da gwamnatin mulkin soji ta Maaouiya Ould Taya a ranar 3 ga watan agusta.