An fara kai taimako ga wadanda girgizar kasar Java ta rutsa da su | Labarai | DW | 27.05.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An fara kai taimako ga wadanda girgizar kasar Java ta rutsa da su

Wata girgizar kasa mai karfin gaske ta lalata gagaruruwa da kauyuka a tsakiyar kasar Indonesia a yau asabar, inda ta halaka mutane sama da dubu 3 yayin wasu dubbai suka samu raunuka. Girgizar kasar ta janyo fargabar aukuwar wani bala´in igiyar ruwa irin na Tsunami. Dubban mutane a cikin dimauta suka yi ta ficewa daga gidajensu zuwa wasu yankuna na tuddai bayan jita-jitar cewa wata igiyar ruwa ta Tsunami ta auku kamar yadda aka samu a cikin watan desamban shekara ta 2004. Kakakin asusun tallafawa kananan yara na MDD wato UNICEF, John Budd, wanda a halin yanzu yake birnin Jakarta ya nuna da cewa da yake sun kasance cikin shirin ko takwana saboda yiwuwar yin aman wuta na dutsin Merari dake kusa, ya sa sun iya kai dauki cikin gaggawa a wurin da aka yi girgizar kasar. Yanzu haka dai asusun UNICEF ya tura da abinci, tantuna, ruwan sha da kuma magunguna zuwa tsibirin Java. Budd ya ci-gaba da cewa:

“A fili ya ke cewar muhimmin abin da ake bukata a yanzu shi ne kula da wadanda suka jikata musamman wadanda raunukan su suka fi yin muni. A Bantul alal misali dubban mutane suka jikata. Saboda haka yake da muhimmanci mu gaggauta kai magunguna da kayan aiki zuwa asibitocin dake yankin. Mun yi maraba da yadda gwamnatin Indonesia ta hanzarta tura ma´aikatan ceto da kuma taimako zuwa birnin Yogyakarta, inda girgizar kasar ta fi yin muni. Ina fata reshen kungiyar Red Cross a Indonesia zata kakkafa asibitocin tafi da gidan ka. Saboda haka ina ganin za´a samu sukunin kai daukin gaggawa ga wadanda suka samu raunuka.”