An fara kai ɗauki ga ƙasar Girika mai fama da bala´in wutar daji | Labarai | DW | 26.08.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An fara kai ɗauki ga ƙasar Girika mai fama da bala´in wutar daji

Taimakon farko daga kasashen waje ya fara isa kasar Girika wadda ke kokarin shawo kan wutar dajin nan dake barazanar cinye yankin tsibirin Peloponnese. Yanzu haka dai jiragen saman kashe gobara 4 daga Faransa da biyu daga Italiya sun isa yankin don taimakawa a kashe wutar dajin. Alkalumman baya bayan nan da hukuma ta bayar na nuni da cewa mutane 51 sun rasa rayukansu yayin da hukumomi ke fargabar cewa wutar ka iya yiwa daruruwan mazauna kauyuka a yankin kudancin kasar kawanya. FM Kostas Karamanlis yayi sanya dokar ta baci tare da zargin cewa wasu ne suka cunna wutar da gangan, wadda a halin yanzu ta ke barazanar cimma garin Olympia mai dadadden tarihi.

Karamanlis:

“Ya al´umar kasar Girika kun san cewa yanzu kasar mu na cikin wani shirin ko-takwana. Saboda haka ina kira gareku da ku hada karfi waje daya don yakar wannan wutar daji da ta addabe mu.”

Kawo yanzu ´yan sanda sun kame mutane 3 bisa zargin hannu wajen tayar da wutar.