An fara kada kuri´a ta tsakiyar wa´adi a Amirka | Labarai | DW | 07.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An fara kada kuri´a ta tsakiyar wa´adi a Amirka

An fara kada kuri´a a zaben ´yan majalisun dokokin Amirka. Fiye da Amirkawa miliyan 200 ne suka cancanci kada kuri´a a zaben inda za´a zabi ´yan majalisar dattijai 33 daga cikin 100 da dukkan ´yan majalisar wakilai su 435. binciken jin ra´ayin jama´a da aka gudanar ya nunar da cewa jam´iyar Democrat ke kan gaban jam´iyar Republicans ta shugaba GWB. Kawo yanzu dai jam´iyar Republicans ce ke da rinjaye a dukkan majalisun dokokin guda biyu. A lokacin yakin neman zaben na karshe da ta yi ´yar majalisar dattawa kuma uwargidan tsohon shugaban Amirka Bill Clinton, wato Hilarry ta yi kira ga masu zabe da su juyawa ´yan republicans baya.

Yakin Iraqi dai ne ya mamaye yakin neman zaben wanda ake yiwa lakabi da na tsakiyar wa´adi.