1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An fara kada kuri´a a zaben ´yan majalisar dattijan Zimbabwe

November 26, 2005
https://p.dw.com/p/BvJM

Masu zabe a Zimbabwe sun fara kada kuri´a don zaben wakilan sabuwar majalisar dattijai da aka kirkiro. Kimanin mutane miliyan 3.3 suka cancanci kada kuri´a a zaben wanda masu lura da al´amuran yau da kullum suka yi hasashen samun yawan mutane da bai taka kara ya karya ba. Hakazalika ana saka ayar tambaya game da rawar da sabuwar majalisar dattijan mai wakilai 66 zata taka. Majalisar zata kunshi sarakunan gargajiya 10 da zababbun wakilai 50 sai kuma mutum 6 wadanda shugaba Robert Mugabe zai nada. Sakamakon rarrabuwar kawuna da aka samu a cikin ta na kauracewa zaben, jam´iyar ´yan adawa ba ta tsayar da ´yan takara a dukkan mazabun da ake takara kai ba. Kasahen duniya sun yi suka ga zaben wanda suka yi zargin cewa wani mataki ne da zai karfafa ikon shugaba Mugabe akan gwamnati.