1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An fara kada kuri´a a zaben shugaban kasar Venezuela

December 3, 2006
https://p.dw.com/p/BuZF
An bude tashoshin zabe a Venezuela inda shugaba mai ci kuma mai matukar adawa da Amirka Hugo Chavez ke neman sabon wa´adin shugabanci na shekaru 6, tare da goyon baya na wani tsarin gurguzu da ya kirkiro. Babban mai kalubalantar sa Manuel Rosales wanda gwamnan wata jiha ne ya ce zai gabatar da tsarin sakarwa harkokin kasuwanci mara idan yayi nasara a zaben na yau. To sai dai dukkan hasashen da aka yi na nuni da cewa Chavez ne zai lashe zaben domin daukacin talakawa da ma´aikata a kasar na goyon bayan shirin sa na yaki da talauci. An girke dakarun tsaro da sojoji kimanin dubu 25 don tabbatar da tsaro a lokacin zaben.