An fara jana’izar ministan ƙasar Lebanon Pierre Gemayel, da aka yi wa kisan gilla shekaranjiya a birnin Beirut. | Labarai | DW | 23.11.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An fara jana’izar ministan ƙasar Lebanon Pierre Gemayel, da aka yi wa kisan gilla shekaranjiya a birnin Beirut.

Rahotannin da ke iso mana daga ƙasar Lebanon sun ce an fara jana’izar ministan masana’antun ƙasar, Pierre Gemayel da aka yi wa kisan gilla shekaranjiya a birnin Beirut. Limaman kirista da jama’a da dama ne suka taru a cocin St. George da ke birnin na Beirut don halartar jana’izar. Wani ɗaya daga cikin masu kare lafiyar ministan shi ma ya rasa ransa a harin da aka kai musu. Magoya bayan ministan dai na zargin Siriya ne da shirya kisan da aka yi masa. Amma tuni Damascus ta yi watsi da wannan zargin. A hlin da ake ciki dai, kwamitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya, ya ba da sanarwar cewa, ya umarci kwamitin da ke gudanad da bincike kan kisan gillar da aka yi wa tsohon Firamiyan Lebanon ɗin, Rafik Hariri, da ya kuma biciki wannan kisan da aka yi wa minista Pierre Gemayel.

Game da halin hauhawar tsamarin da Lebanon ta faɗa ciki bayan kisan gillan da aka yi wa ministan, Babban Sakataren Majalisar Ɗinkin Duniya Kofi Annan ya bayyana cewa:-

„Na tuntuɓi shugabanin ƙasashen yankin, a cikinsu har da na Siriya da Iran, da su ba da haɗin ka kafofin Lebanon ɗin, don tabbatad da cewa an sami zaman lafiya da kwanciyar hankali a ƙasar. Ina fata dai gwamnatocin duk ƙasashen da muka tuntuɓin, za su amsa kiran da muka yi musu cikin gaggawa, don mu iya ɗaukan mataki na gaba. Babu shakka, ana cikin wani mawuyacin hali. Sabili da haka ne ya kamata mu yi duk iyakacin ƙoƙarinmu wajen taimaka wa al’umman ƙasar Lebanon da gwamnatinta don su sami haɗin kai a dun faɗin ƙasar.