An fara janaízar mutanen da suka rasu a zabtarewar kasa a Phillipines | Labarai | DW | 19.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An fara janaízar mutanen da suka rasu a zabtarewar kasa a Phillipines

Alúmar kauyen Leyte a kasar Philippines a yau suka fara janaizar dangi da yan uwan su da suka rasu a sakamakon zabtarewar kasa. Kimanin mutane 1,800 ne ake kyautata tsammanin sun riga mu gidan gaskiya a ruftawar kasar. Gwamnan lardin kudancin Leyte Rosette Lerias ya baiyana cewa a yanzu haka an janaizar mutane 50 wadanda aka binne su a kabari guda. Maáikatan ajagi dake aikin tono mutanen da kasar tarufta da su sun fidda tsammanin samun wadanda suka saura da rayukan su a rubtawar kasar. Maáikatan agaji nafuskantar matsaloli saboda chabewar laka a sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya. Mahukunta a yankin sun yi gargadin cewa akwai yiwuwar sake aukuwar rubtawar kasar a sakamakon ruwan saman da kuma laushi da kasar ta yi.