1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An fara gudanar da bukukuwan shiga sabuwar shekara a wasu yankuna na duniya

An gudanar da bukukuwan shiga sabuwar shekara a yankin Pacific da kasashen Australiya da kuma New Zealand. Kimanin mutane miliyan daya ne suka hallara a kewayen tashar jirgin ruwan birnin Sydney don gudanar da wasan wuta na shiga sabuwar shekara ta 2006. An dai tsaurara mamatakan tsaro bayan tarzomar da aka fuskanta kwanan nan a unguwannin dake wajen birnin. A Japan ma kamar yadda aka saba a bikin sabuwar shekara wannan karon ma mutane da dama sun hau kan tsaunuka don jirar sabuwar shekarar. A nan Jamus kuwa a dandanlin Brandenburg Tor za´a gudanar da gagarumin bikin shiga sabuwar shekarar. A cikin jawabin ta na farko na sabuwar shekara da aka nuna ta gidajen telebijin kasar, SGJ Angela Merkel ta yi kira ga ´yan kasar da su yi aiki tukuru wajen sabunta kasar ta Jamus.