1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An fara girke sojojin Libanon a kan iyakarta da Isra´ila

A karon farko sojojin Lebanon sun fara kafa sansanin a kan iyakar kasar da Isra´ila. Tare da taimakon sojojin MDD a yau dakarun Libanon su kimanin 200 sun isa yankin kan iyakar tsakanin kasashen biyu. Girke dakarun a yankin da ake yiwa lakabi da shudin layi, na daga cikin sharudan da Isra´ila ta gindaya na kawo karshen farmakin da take kaiwa mayakan Hisbollah a kudancin Libanon. A jiya juma´a shugaban Hisbollah Hassan Nasrallah ya fadawa wani taron gangami na dubun dubatan magoya bayansa cewa ba zai kwance damarar mayaknsa ba. Ya ce yanzu haka Hisbollah na da rokoki sama da dubu 20.