An fara ganin alamar lafawar kurar rikici a yankunan Falasdinawa | Labarai | DW | 13.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An fara ganin alamar lafawar kurar rikici a yankunan Falasdinawa

Ana samun ci-gaba a kokarin da ake yi na kafa wata gwamnatin hadin kan kasa tsakanin Falasdinawa. Rahotanni daga Ramallah sun yi nuni da cewa wakilan shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas da shugaban Hamas Khaled Mashaal sun samu wasu nasarori a tattaunawar da suke yi a Syria. Yanzu haka kuma wasu wakilai biyu na majalisar dokokin Falasdinu sun isa birnin Damascus don ci-gaba da wannan tattaunawa. A kuma halin da ake ciki, FM Falasdinawa Isma´il Haniya ya yi kira ga kungiyar Hamas da ta Fatah da su kawo karshen tashe tashen hankula da suke yi da juna, wanda kawo yanzu yayi sanadiyar mutuwar mutane kimanin 30. A wani labarin kuma kungiyar ma´aikatan gwamnati ta kawo karshen yajin aikin wata 4 da ´ya´yanta ke yi saboda rashin biyan albashinsu. Wata yarjejeniya da suka kulla da hukumar mulkin cin gashin kan Falasdinu, ta tanadi biyan su albashin wata daya nan take.