An fara azumin watan Ramadan a wasu ƙasashen musulmi | Labarai | DW | 12.09.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An fara azumin watan Ramadan a wasu ƙasashen musulmi

Yau a wasu ƙasashen musulmi na dunia a ka fara azumin watan Ramadan.

Rahottani daga Nigeria da Niger sun tabbatar da cewar mafi yawan musulmi a wannan ƙasashen sun tashi da azumin farko a yau laraba.

Saidai a ƙasar Indonesia, wadda ta fi yawan musulmi a dunia, da kuma wasu ƙasashen larabawa, da su ka haɗa da Saudi Arabia , Koweit, Bahrein, Qatar, da haɗɗaɗiyar Daular larabawa, sai gobe a ke fara azumin na Ramadan.

Kamar ko wace shekara, an ka samu rabuwar kanu a game da farkon wannan wata mai tsarki na addinin musulunci.