1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An fara aikin sabunta Rajistar masu zabe a Nigeria

October 25, 2006
https://p.dw.com/p/Bueb

Hukumar zabe ta Nigeria ta fara aikin sabunta rajistar sunayen masu kada kuriá a yau laraba domin share fage na zabe mai zuwa a watan Aprilun shekara ta 2007. A karon farko a tarihin kasar, zaá yi amfani da naurar Computer wanda ake fatan zai taimaka wajen rage magudin zabe da kasar ta shahara a kai. Hukumar zaben tace dukkan wanda aka kidaya zaá sanya hoton sa dana yan yatsun sa a katin naura mai kwakwalwa wanda zaá yi amfani da shi wajen kada kuriá. Wani jamiín hukumar zaben a Abuja Nick Dicson yace a baya an rika samun mutane wadanda su kan yi rajistar sau da dama da yin sojan gona da zuren kuriú har kuma da sayen katunan zabe. Yace a wannan karon hakan ba zai yiwu ba. Sai dai kuma tun baá je ko ina an fara samun matsaloli da naurar Computer ta kidaya,