1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An dakile yunkurin juyin mulkin Turkiyya

Usman Shehu UsmanJuly 16, 2016

Al'ummar Turkiyya ta taka muhimmiyar rawa wajen dakile yunkurin juyin mulkin da kimanin mutane 265 suka mutu wasu 1,440 suka jikkata bayan da wasu sojojin suka so kifar da gwamnatin shugaba Recep Tayyip Erdogan.

https://p.dw.com/p/1JPwW
Hoto: Getty Images/AFP/A. Altan

Shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan ya fadawa 'yan kasar cewa gwamnatinsa na yin aiki da duk karfin da take da shi don murkushe juyin mulkin da aka so yi masa a daran jiya. Akalla mutane 90 suka muta bayan barin wuta da aka yi ta sama da ta kasa, a manyan biranen kasar ta Turkiya wato Ankara, babban birnin kasar da kuma Istanbul cibiyar kasuwanci. An dai kwana ana jin fashewar ababai a biranen, kuma gidan talabijin din kasar aka bayyana cewar, kimanin mutane 1,154 a yanzu haka suka jikkata. A fadar gwamnatin dai juyin mulkin bai yi nasara ba, domin talakawan Turkiya sun bazu kan tituna suka yi ta arangama da sojojin da ke son juyin mulkin, abin da ya karya lagwan sojojin.

Sai dai jin fashewar bama-bamai a harabar majalisar dokokin har izuwa safiyar yau, ya kawo dan shakku bisa halin da ake ciki. Yanzu dai shugaba Erdogan ya dawo Istanbul daga woni hutun da yake yi, kuma ya bayyanan cewar shi ne ke iko da kasar, yayin da sojoji da jami'an leken asiri da ke masa biyayye ke kan farautar sojojin da suka shirya juyin mulkin. An dai tsare sojoji da dama daga cikin wadanda suka shirya juyin mulkin a yanzu haka.

Kawo yanzu dai kasashen duniya sun fara mayar martani kan yunkurin juyin mulkin na kasar Turkiya, inda aka jiyo Donald Tusk shugaban hukumar Tarayyar Turai yana mai cewar. "Turkiya babbar gawa ce ga Kungiyar Tarayyar Turai. Tarayyar Turai na baBda cikakken goyon baya ga gwamnatin da aka zaba bisa ta farkin demokradiyya da sauran dokokin kasar Turkiya. Muna kira cikin gaggawa a maida Turkiya bisa tsarin mulkinta. Za mu ci-gaba da bin diddigin halin da ake ciki a Turkiya, bisa aiki tare da kasashe 28 mamabobin EU"