An dakatar da jam'iyyun adawa don ingiza tarzoma
February 8, 2018Talla
Matakin gwamnati ya biyo bayan zanga zangar kungiyoyin kwadago da jami'yyun suka jagoranta dangane da matakin tsuke bakin aljihu na gwamnatin.
Acewar ministan tsaron Chadin Ahmat Mahamat Bachir, an dakatar da ayyukan jam'iyyun na tsawon watanni biyu, saboda abun da ya kira dalilai na tsaron kasa.
Daura da haka hukumomin kasar sun sanar da haramta jerin gwano da ake shirin yi akan tituna a wannan Alhamis a karkashin jagorancin kungiyoyi masu zaman kasansu da na kwadago da jam'iyyun adawa.