1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An dakatar da aikin agaji a wasu yankuna biyu na Kashmir

Majalisar Dinkin Duniya ta ce ta dakatar da aikin ba da taimako a wasu yankuna biyu dake bangaren Pakitsan a lardin Kashmir wanda ke fama da masifar girgizar kasa. MDD ta dauki wannan mataki ne bayan da wasu kauyawa suka farma jiragen samanta masu saukar ungulu a wannan yanki. Su dai kauyawan sun nemi a kwashe su ne daga yankin. Wani kakakin MDD ya ce za´a katse dukkan jigilar kai agaji ta sama zuwa yankin Lipa don tabbatar da tsaro da lafiyar ma´aikata da kuma matukan jiragen saman masu saukar ungulu. Mutane fiye da dubu 73 suka mutu yayin da miliyoyi suka yi asarar gidajensu sakamakon mummunar girgizar kasar da ta auku a yankin a cikin watan okotoban bara. Yanzu haka dai miliyoyin mutane na zaune ne a cikin wani yanayi na matsanancin sanyin hunuturu karkashin tantuna da aka kakkafa.