An dago yunkurin kai hari a Jamus | Labarai | DW | 22.01.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An dago yunkurin kai hari a Jamus

'Yan sanda sun cafke wani mutumi wanda ake tsare da shi, bisa zarginsa da yunkurin kai hari a Jamus.

'Yan sanda a Jamus sun kama wani mutumi wanda ake zargi da shirin kai hare-hare na ta'addanci, kamar yadda wata mujalla ta FOCUS ta ambato.Yanzu haka ana tsare da mutumin a garin Neuss da ke a yammacin kasar. 'Yan sandan sun kwace wayoyin salula da na'urar Computer mallakar mutumin kana kuma an yi wa mai dakinsa tambayoyi. Nan gaba za a samu cikakken bayani dangane da halin da ake ciki.