An dage zaben shugaban kasa a Ivory Coast | Siyasa | DW | 09.09.2005
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

An dage zaben shugaban kasa a Ivory Coast

Sakatare general na Mdd ya sanar da dage zabe saboda rashin shiri

default

Sakatare general na MDD Kofi Annan ya bayyana rashin yiwuwan gudanar da zaben shugaban kasar Ivory Coast ranar 30 ga watan Oktoba kamar yadda aka tsara a baya.

Babban jagoran na majalisar dunkin duniya ya fadawa gidan radion birnin Paris a jiya alhamis cewa,akwai batutuwa da dama da zasu jinkirta wannan zabe na shugaban kasa,musamman rashin isasshen shri ,da kuma takunkumin kasashen ketare wa bangarorin biyu dake yaki da juna.

Mr Annan yace har yanzu shugabannin jamiiyyun day an siyasa sunki bada hadin kan daya dace ,kana har yanzu babu daya daga cikin kaidojin gudanar da zabe da aka cimma ,wadanda suka hadar da kafa hukumar zabe .Kuma babu yadda zaa gudanar da wannan zabe na ranar 30 ga watan gobe idan babu cikakken shiri.

Yace bisa dukkan alamu komitin sulhun majalisar zata dauki matakai a dangane da takunkumi wa bangarori biyu dake yakan juna a kasar ta Ivory Coast.

Shima jakadan Mdd na musamman dangane da wannan zabe,ya fadawa manema labaru cewa babu yiwuwan gudanar da wannan zabe kamar yadda aka shirya a baya.

Jakada Antonio Monteiro yace tsayar da rana domin gudanar da zaben ba shine abu mafi muhimmanci ba amma,irin shiri da zaayi na tabbatar dacewa an samu gudanar da zaben ta hanyar data dace. Bugu da kari yace dole ne su samu sunayen yan kasar ta Ivory coast da suka cancanci kayat da kuria,wanda zaizo daidai dana jamiiyyun siyasar kasar.

Yanzu haka dai yan adawa da magoya bayan gwamnatin kasar dai bias dukkan alamu sun nuna halin ko oho dangane da wannan matsayi da mdd ta gabatar n adage wannan zabe,bayan cece kuce kan dokokin zabe da batutuwa na cikin gida.

A kasa dake da baki masu yawan gasket dake zama cikinta,kana a bangare guda wadda arewacinta keda mafi yawan alummar musulmi,wadanda suka jima suna kukan wariya,daga kudanci dake da alumma mabiya addidinin christa,matsalar mallakar yancin kasancewa dan asalin Ivory coast ,musamman dangane da yancin zabe ya haifar da matsala babba.

Ayanzu haka dai kalilan ne daga cikin yarjejeniyar da aka cimma ake aiki dashi,kuma babu jerin sunayen masu zabe balle hukumar gudanar da zaben,kana yan tawayen kasar suna masu cewa kowace gwamnati zaa kafa a Ivory coast din ,ba zasu lamunci kasancewar shugaba Laurent Gbagbo bay a kasance cikinta ba.

A makon daya gabata nedai shugaba Gbagbo ya gabatar da wasu sabbin dokoki na kasa da suka hadar da harkokin zabe,bayan yan adawa sunyi watsi da mafi yawa daga cikin wadannan dokokin.

Jakadan Mdd Monteiro wanda aka nada a watan yuli domin kula da zaben ,yayi fatan cewa cikin mako mai zuwa zaa cimma nada hukumar zabe mai zaman kanta,wadda zata fara aiki cikin gaggawa.

Tun a shekara ta 2002 nedai Ivory coast mai albarkatun cocoa a yammacin Afrika ta fada rikicin siyasa,wanda ya dare ta biyu,da arewacin kasar a hannun yan tawaye ,ayayinda kudanci ke hannun gwammnati a karkashin shugaba Laurent Gbagbo.

 • Kwanan wata 09.09.2005
 • Mawallafi Zainab a Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvZp
 • Kwanan wata 09.09.2005
 • Mawallafi Zainab a Mohammad
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/BvZp