An dage yajin aiki a Guinea | Labarai | DW | 28.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An dage yajin aiki a Guinea

Shugabannin kungiyoyin maaikata na Guinea sun dage yajin aiki na kasa baki daya da suka gudanar a fadin wannan kasa,sakamakon cimma yarjejeniya da shugaban kasar Lamsana Conte ,na nadin premier wanda alummomi zasu amince dashi,tare da rage farashin man petur dana shikafa.A yayin wannan yajin aikin kasa baki daya na tsawon kwanaki 18 a kasar ta Guinea dai,arangama tsakanin masu adawa da gwamnati da jamian tsaro ,ya haddasa mutuwan mutane 59,a hukumance.Sakamakon wannan yajin aiki ne dai aka dakatar da sarrafa sinadran Aluminiumm,wanda sai jiya aka fara gudanarwa.Saidai kawo yanzu baa fara jigilarsu ba daga tashar jiragen ruwa dake garin Kamsar.Shugaba Conte wanda ke kann karagar mulkin Guinea dake yammacin Afrika,tun da 1984 dai,ya fuskanci fushin alumomin wannan kasa sakamakon rashin aikinyi da tsadar rayuwa.