1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An dage shari´ar Saddam Hussein uwa ranar laraba

January 29, 2006
https://p.dw.com/p/BvAM

Tsohon shugaban Iraqi Saddam hussein ya fice daga zauren kotun da ke masa shari´a mintoci kadan bayan an koma ga sauraron shari´ar a karkashin jagorancin sabon alkali. Hakan dai ya zo ne bayan da alkali Raouf Abdel-Rahman ya umarci dan´uwan Saddam Hussein wanda shi ma akewa shari´a Barzan Ibrahim hassan al-Tikrit da ya fice daga kotun bayan ya kaddamar da wani dogon jawabi duk da hana shi yin haka da alkalin yayi. Su ma lauyoyin dake kare Saddam Hussein sun fice daga zauren kotun jim kadan bayan haka. An shiga wannan hali ne sakamakon wani zazzafin kace-nace da ya auku tsakanin Saddam da alkalin kotu. Tsohon shugaban na Iraqi yayi zargin cewa kotun ta Amirka ce amma alkalin ya dage cewar kotun ta Iraqi ce saboda haka tana da ´yancin yi wa Saddam da sauran mukarrabansa shari´a. Wani labarin da ya iso mana yanzu ya rawaito alkalin na cewa an dage zaman kotun har zuwa ranar laraba mai zuwa.