1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An dage lokacin yanke hukuncin mika Hissane Habre ga kasar Belgium

November 22, 2005
https://p.dw.com/p/BvJx

Daya daga cikin kotun daukaka kara a kasar Senegal tace a ranar juma´a ne mai zuwa zata yanke hukunci akan bukatar da kasar Belgium ta gabatar mata.

A can baya dai da an shirya cewa a yau ne kotun ta Tschad zata yanke wannan hukunci.

Kotun dai ta Belgium ta bukaci da a mika mata tsohon shugaban kasar Tschad ne wato Hissane Habre dom amsa laifuffukan da ake tuhumar sa da aikatawa.

Wadan nan laifuffuka dai sun shafi kisan cin zali ne dake da nasaba da siyasa da kuma take hakkin bil adama a lokacin mulkin sa da yayi a tsakanin shekara ta 1982 izuwa 1990.

Tuni dai lauyoyin dake kare shugaba Habre suka karya wannan zargi da cewa tsohon shugaban bai san dasu ba.

Rahotanni dai sun shaidar da cewa, kotun ta Belgium ta mika wannan bukatar ne bisa bukatar yin hakan da wasu yan kasar dake da asali da kasar ta Tschad suka mika mata a karkashin dokar data tanadar da yin hakan.