An dage dokar Talala a kasar Iraqi | Labarai | DW | 27.02.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An dage dokar Talala a kasar Iraqi

Yayin da a yau aka dage dokar takaita zurga zurgar jamaá dana ababen sufuri a kasar Iraqi, rigingimu tsakanin mabiya dariku na cigaba da aukuwa bayan da a makon da ya gabata harin bom din da aka kai a wani masallaci na yan shiá a garin samara haifar da matsanancin tashin hankali duk da kiran da shugabannin addini dana siyasa ke yi na a sami zaman lafiya. A jiya lahadi rahotanni sun baiyana cewa mutane 30 ne suka rasu bayan wasu hare hare a birnin Bagadaza. A garin Hilla wani bom da ya fashe a cikin wata karamar mota ya yi hallaka mutane biyar. A kuma garin Bakuba yan bindiga dadi sun bude akan wasu yara kanana inda biyu daga cikin su suka riga mu gidan gaskiya. Hukumomin sojin Amurka sun sanar da mutuwar wasu sojojin su uku a wani harin kwantar bauna a garin Bagadaza. A waje guda kuma malamin nan mai tsatsaurar raáyi Moqtada al Sadr ya bi sahu wajen yin kira domin tabbatar da hadin kan alúmar kasa.