1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

An dage dokar ta baci a kasar Georgia

Mahukunta a ƙasar Georgia sun sanar da ɗage dokar ta ɓaci da su ka kafa kwanaki Tara da su ka wuce.Bayanin hakan ya fito ne daga ma´aikatar kula da harkokin cikin gida ta ƙasarne. Ɗaukar matakin nada nasaba da kaɗa kuri´ar ɗage dokar ne da´ Yan Majalisun dokokin ƙasar su ka yi ne a jiya. An dai kafa dokar ta ɓacinne a ranar bakwai ga watannan, bayan da ´Yan adawa su ka gudanar da zanga zangar bore da Gwamnati. Masu zanga zangar dai na bukatar murabus ɗin shugaba Saakashvili ne tare da gudanar da zaɓe a ƙasar. A waje ɗaya kuma shugaba Saakashvili ya naɗa Mr Lado Gurgenidze, a matsayin sabon Faraminista. Kafin naɗin na sa Mr Lado mai shekaru 36, na riƙe da muƙamin shugaban babban Bankin ƙasarne.